Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 46


Farhatal Qalb 46
Viral

PG:46_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_

_
*Knocking* kofar suka fara yi. Kafin kararrawa (door bell) ta fara kara. Ya tashi ya nufi wajen kofar. Yana mai waiwayon kafar bene ko Ahlam zata sakko.

Shiru shiru ba alamun ta. Kawai yasa hannu ya bude kofar. Suka shigo ciki. Haj Hameedah da Haj Aisha sai Ummimi kakar su. Da Umma Hadiza data shiga a karshe.

“Ahh mazan fama…..” Ummimi kakar su ta fada tana dashare hakoranta.

Ya saka hannu ya sosa keyar sa yana murmushi.

“Sannun ku da zuwa….” Ya fada cikin girmamawa.

Wuce shi sukayi. Suka zazzauna akan kujeru. Ya yinda Umma Hadiza ta nemi waje daga kasa ta zauna.

“Ah haba Hadiza. Dan Allah tashi ki zauna akan kujera.”

“Tashi mana …”

“Tashi ‘yar nan ki zauna…..”

Haj Hameedah…Haj Aisha da Ummimi suka shiga bai wa Umma Hadiza umarni kan ta tashi daga zaunen da take ta koma kan kujera.

Umma Hadizan ta zauna daga gefen wata kujera kanta a kàsa.

Ya yin da Zayn ya tsugunna ya shiga gaishe su daya bayan daya cikin girmamawa da mutuntawa.

“Ina Ahlam dinne….?”

“Ta… Tana sama yanzu zata sakko.”

Waheedah ta futo daga cikin dakin da tayi sallah. Ta tsugunna ta gayshe su. Umma Hadiza sai murmushi take

“Sannu da kokari Waheedah… Allah ya saka da alkhairi.”

“Amin Maa..”

Sun dan yi mintuna da zama. Shiru ba Ahlam. Sai can daga baya ta sakko daga ita sai dogon hijabi zuwa gwiwa. Kayan baccin ta na dazu ta mayar .

Mamakin hakan ya mamaye Zayn. Har ya kasa boye halin da yake ciki a fuskar sa.

Zama tayi akan kujera tanata murmushi

“Ina wunin ku??. Ummimi na, Maa da Aunty Ai…”

Suka amsa. Ya yinda ta juya ta kalli Umma Hadiza.

“Ina wuni?”

“Lapia kalau amarya.”

Can dai sunata zaune jugum. Waheedah ta miqe ta shiga kitchen din. Ta shiga dakko trays da plates da cokula da serving spoons.

Ta koma ta dakko warmers na abincin ta ajiye musu akan dinning dake gefen parlorn.

Ta sake bude freezer ta debo musu ruwa da lemo ta ajiye.

“Ahh .. Har na manta ma… Sannu sis.” Waheedah ta fada.

Haj Hameedah na hankalce da su. Ta dubi Zayn da ke gefe, Kan sa akan tv. Ya yin da Ahlam ke danne danne a wayarta.

“Maa ga abincin can kar ya huce.”

“Toh Waheedah sannu da aiki kinji?”

“Yauwa…”

Miqewa sukayi suka nufi dinning din. Ita dai Umma Hadiza bata tashi ba.

“Zo mana Hadiza..”

“Hajia nan din ma yayi ..” ta amsa ta cikin ladabi.

Kan dinning table suka nufa. Suka ja kujeru suka zazzauna.

Ahlam tayi serving dukkanin su abincin.

“Waheedah zo ki zuba… Ki zubawa Umman ku ma”

“Tohm.”

Karasawa tayi dinning din. Ta janyo plate babba ta zuba musu abincin ita da Umman ta.

“Ki kara muku mana…”

“Ya ishe mu haka….”

Ta koma can inda Umman tasu ke a zaune ta ajiye plate din abincin a gaban Umman .

“Sakko muci Umma…”

“Tohm Waheedah…”

Kasan carpet suka zauna. Abincin na tsakiyar su. Su kayi basmala suka fara ci.

Zayn na kan kujera ya kurawa tv kallo.

“Ah ina naka abincin? Zuba ma sa yaci Ahlam.”

“Na koshi Ummimi.”

“Dan Allah ka karba ka ci ka ji?”

Zai sake cewa wani abun . Haj Hameedah ta masa kallon kar ya yi haka. Ya dan kakaro yake yace,

“Toh..”

“Yauwa… Sannu Ahlam da aiki. Abinci yayi dadi.” Ummimi ta fada tana mai sake yanko loma ta saka a bakinta.

Ahlam din ta danyi yake. kafin tace,

“Ai bama ni nayi ba Ummimi.”

“Ai ho to… Na wajen sayarda abinci ne?”

“Ah’ah Waheedah ce ta yi komai…” Ta karasa fada hadi da sa ka hannu ta nuna Waheedah da yatsanta.

“Ah masha Allahu… Lalle tayi kokari.”

“Sosai ma. ” Cewar Hajia Aisha.

Ita dai Haj Hameedah murmushi kawai ta ke.

Ahlam ta zuba abincin a plate ta kai gaban Zayn. Yana daga zaune ta tsaya akan sa kerere. Da plate din abincin tamkar zata dora akan sa

“Gashi….” Hannunta daya na kan wayarta . Dayan kuma tana miqa masa abincin saura kadan ya bare.

Ya sa ka hannu ya karbi abincin ya ajiye a gefe. Kallon abincin ya tsaya yi. Gashi dai komai tsaf tsaf. Kamshin abincin na ta dukan kofofin hancin sa.

Amma tsantsamin sa da kuma aqidar sa ta qin cin abincin da ba na Maa ba yasa ya kauda fuska kawai yana jan kasan leben sa.

Ahlam ta koma ta zauna akan kujera tanata scrolling pages a Instagram. Sai bude videos take yi tana kalla.

Waheedah ta tattare inda suka ci abincin ta kai kitchen. Su Maa na karasa ci ta gyara wajen ta kai kwanukan kitchen tana dauraye wa.

“Wai baka ci abincin ba ka barshi yanata sandarewa?”

‘Zan ci…..” Ya fada ahankali yana mai kallon idanun Haj Hameedah mahaifiyar su.

Cokalin ya dauka ya saka acikin abincin. Sai yamutsa fuska yake. Amman tunda ya fara taunawa sai yaji wani dadi da gardi na fita na abincin.

Ya samu kan sa da sake ciko loma ya saka a bakin sa. Tabbas gaskia ne ba mafarki yake ba. Bai taba cin abincin mutane me dadi irin wannan ba idan har ka tsame na mahaifiyar su Haj Hameedah.

Ya shiga zura loma bayan loma yanata ci. Yana korawa da lemo. Sai daya cinye tas tukun sannan ya ajiye plate din yana goge bakin sa da tissue.

“Alhamdulillah…” Ya fada yana sake shan ruwa.

Waheedah ta sake fitowa daga kitchen tanata dauke kwanukan da bata dauka ba dazu. Ta hada da wanda ke agaban Zayn . Kitchen ta kai su ta wanke su tas. Tatattare kitchen din . Ko’ina tsaf. Sai da ta tabbatar ta gyara komai sannan ta koma dakin nan ta shiga bandaki ta watsa ruwa.

Ta mayar da kayan makarantar ta. Rigar Kuma ta ninke ta dauka ta fita daga kitchen dakin ta koma parlorn. Daga gefe ta tsugunna.

“Mu tafi ko…?” Ummimi ta fada tana kallon Haj Hameedah.

“Tohm Ummimi yadda kika ce.”

Mikewa suka yi baki daya. Ciki harda Waheedah dake gyara zaman rigar hannun ta.

“Sis ga kayan. Nagode.”

“Wane kaya?”

“Rigar da kika bani na saka nayi aiki da ita..”

“Oh . Ni ba aro na baki ba Waheedah… Kyauta na ba ki.. kinji ko?”

“Eh. Nagode Allah ya saka da alkhairi ya kara miki arziki mai tarin albarka Amin. ”

“Amin…”

Zayn yana sauraron maganganun da su ke. Yanata mamakin adduoin da Waheedah ke yi.

Ya danyi murmushi kawai kansa akan tv.

Waheedah ta matsa wajen Haj Hameedah tana gaya mata alkhairi da Ahlam ta mata na bar mata kayan da tayi.

“Tohm Ahlam godia muke… Waheedah tace na miki godia.”

“Kai ba komai Maa. Ai an zama daya.”

“Angode kwarai. Allah ya saka da alkhairi.” Cewar Umma Hadiza dake yaba kyautar.

“Amin.”

Fita sukayi dukkanin su wajen. Direban ya tashi motar. Suka shiga baki dayan su.

Ya yin da Ahlam da Zayn ke ta waje a tsaye suna musu sallama . Har suka fice daga gidan tukun sannan Ahlam ta juya ta shiga ciki.

Zayn ya bita a baya shi ma. Ko da ya shiga bata parlorn. Ba kuma ta kasan baki daya.

Saman ya haye da sassarfa. Ya bude dakin ta ya leka. Tana kwance akan gado kamar ruwa.

Tayi dai dai da ita. Hijabin na gefe. Ita kuma ta sake barrarrajewa akan gadon bayan ta tukwikwiye jikin ta da bargo.

Rufo mata kofar dakin yayi. Ya koma kasa ya zauna akan kujera. Tv nata yi. Idanun sa na kan tv. Amman zuciyar sa ta tafi duniyar tunani. …..

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply