Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 44


Farhatal Qalb 44
Viral

PG:44_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_

___
*Ta* riqo butar itama. Suka shiga ja in ja… Sai data bari inna Sa’adatu ta riqe butar da karshen karfin ta. Sai ta saki riqon ita da tayi

Inna saadatun ta bugu da bango. Da sauri ta dafe goshinta da hannu saboda radadin zugin da ya fara mata na zafi.

Deluwa tayi murmushi tana girgiza kai . Cikin fushi inna Sa’adatu tace,

“Baqar muguwa. Aniyar ki ta bi ki.”

“Mena miki na mugunta anan? Meye sunan ki ma? Yauwa Sa’adatu. kece muguwa.. Da kika dauki kwabin danwake na kika zubar. Wannan kazamar butar taki zan dauka nayi me da ita? Marka ce ta kawo . Kuma baa mayarda hannun kyauta baya shi ya sa ban ki ba. Na karba na ke rage wutar da ita. Sam bakya abu da hankali.”

“Kece bakya abu da hankali.. Shashasha.” Inna saadatu ta fada tana sakin tsaki

Deluwa ta taka daga inda take zuwa wajen da Inna Sa’adatu ta ke. Ta saita ta ta saki murmushi kawatacce . Sannan tace,

“Da kika zubar da kwabin danwake na nace miki wani abun?”

“Yo me kika isa kice? Ai kece baki da gaskiya.”

Deluwa ta sake shekewa da dariya wannan karon harda tafa hannuwan ta.

“Duk bakaken maganganun da kike fada da sirikar ki Marka kike ba ni ba ”

Inna Sa’adatu taja tsaki. Fuska a murtuke tace,

“Matsoraciya… Gafara can na wuce…”

“Ni nasan hakki da mutuncin manya a tattare da ni. Sa’ar Marka kawai kika ci. Amman ki jira ramuwa ta. Zata baki madaukakin mamaki. ”

“Ke matsa can. Wai akace banza girman mahaukaci. Karamun mai wayo ya fishi… Banason sakarci. Ba kuma na bata lokaci na ga sakarkaru.”

“Zaki ga sakarkaru da idanun ki … Babban labari ne da zaki raina wayon ki…”

Mtssss…. Inna Sa’adatu ta sake jan dogon tsaki ta shige cikin dakin ta . Tana mai wake-wake.  Ya yin da Marka ta shiga bawa Deluwa hakuri.

“Laa bakomi Marka…. Karki damu dan Allah. Wannan din ba rabo bane. Ko da anci sai an amayar.”

“Duk da haka dai . Kiyi hakuri dan Allah. Lefi na ne.”

“Ya wuce Allah….”

Ta tattare wajen. Ita kuma ta Deluwa ta shiga zubawa wadanda suke kaan layi da suka saya. Saura kuma ta basu hakurin kwabin danwaken ya zube.

×××××

Tashin Zayn kenan daga bacci tun bayan da yayi sallar asubah. Bandaki ya shiga ya tara ruwa a kwamun wanka. Turaren wankan da mahaifiyar su Haj Hameedah ta bashi ya dauka ya zuba acikin kwamun wankon (bathtub)

Tsayawa yayi yana karanta rubutun jikin robar turaren na kamfanin turarukan (yerwa incense and more). Ya shaki kamshin yana lumshe idanun sa.

“Oud oudi Bath khumrah….” Ya karanta rubutun jikin robar .

Wankan ya shiga yanayi. Yana karasawa ya zura bathrobe ajikin sa. Dayan hannun sa kuma yana dauke ne da karamun tawul yana mai goge kansa dashi

Sannu ahankali haka ya shiga shiryawa. Ya shafa mai ya goga antiperspirant. Ya fesa turaruka kala kala.

Ba kadan ba kananun kayan da ya saka sunyi matukar futo da zatin haibar kamalar sa. Domin Zayn dan gayu ne na bugawa a jarida. Gashi mekyau masha Allah.

Ya yi shigar jeans da wata long sleeve shirt blue ta Armani. Hannun sa dauke da agogon Rolex da azurfa a yatsan sa daya .

Kasa ya sauka bayan ya taje sumar kansa da comb. Hannun sa rike da ipad dinsa. Ya sauka kasan cikin takun kasaita na masu jini a jika .

“Ahlaam…. Ahlam…. Ahlam…” Ya shiga kiranta yana sake nanata sunayenta a karo na uku.

Shiru ba amsa. Ya leka kitchen bata nan ma. Dayan parlorn da ke a kusa da wani karamin garden ya nufa.

Tun daga bakin kofar yake jiyo sautin maganar ta. Har zai shiga kuma sai ya fasa. Don bayaso yayi interrupting calls dinta.

Juyowar da zai yi ya jiyo ta bayan ta gama kyalkyala daria

“Wallahi nake gaya miki .. wallahi ke ba yadda na zata bane. Ina gaya miki ya rude sosai. Ba inda Zayn bai kissing ba a jiki na.  Ya sa ka hannu z …”

Bai bari ya kara sa ji ba ya juya da sauri ya koma da baya da baya. Akan matattakar kafar bene na biyu ya zauna.

Mamaki da takaici ne ya cika shi. Na jin baki daya yadda suke raya sunnah Ahlam ta kwashe tana gayawa kawarta. Komai da komai ba dadin sauraro ma.

Tamkar ya tashi ya shiga ya lakada mata na jaki haka zuciyar sa ke hasaso masa. Ya danne kawai saboda abunda zai je ya dawo. Ya miqe kenan sai ga futowar ta daga parlorn.

Sanye take cikin pajamas (kayan bacci) kanta ba dankwali . Sumar gashin ta yalwatacciya ta bayyana.

Ta kalle shi ta sake kallon sa tana langabar da kai.

“Ina zaka je haka? .. Sai wani kamshi kake ”

Yayi yake kawai kafin ya ce da ita,

“Ba gaisuwa…?”

Baki ta turo gaba. Ta koma kan wata kujera ta zauna.

“Naga mun zama daya. Gida daya . Kai de kanason gaisuwar nan.   Ni mantawa na ke ”

“To banda abinki ai dole ne ki dinga gaishe ni. Kiyi tunani mana Ahlam.. ko ba aure a tsakanin mu ai a sama nake da ke. Ni Yaya ne a gare ki kar ki manta..”

“Ina kwana?” Ta gayshe da shi kasan maqoshi

Bakinta ya kalla ya gano gaishe shi tayi. Bai amsa ba ya wuce kai tsaye wajen dinning.

As usual ya daga tea flask ba komai aciki. Ya wuce kitchen ma kamar ko da yaushe babu abinci. Ransa ya kai kolokuwar baci. Ya danne dakyar yace da ita,

“Ba abinci …?”

Ta daga kanta . Kafin tace,

“Akwai bread … Ko na dama maka custard ? ”

“Ahlam me na ce miki jia? Da shekaran jia waçcen? Ina ga kullum se na miki maganar nan… Amman sam kinki yi. Tun dazun me kike a kàsa?”

Ta sake yamutsa fuska tana turo bakinta gaba.

“Ai na gaya maka….. Ka dinga hada breakfast dinki. Kai picky eater ne. ”

“Ahlamm… Fisabilillahi kusan kullum abincin daya ne. Indomie, sandwich , bread . Coffee. Ko fruits.. Tunda aka kawo ki gidan nan baki taba girka komai ba..”

“Ina dama maka custard mana… ” Ta amsa ba tare da wata damuwa ba.

Yaja kasan lebensa yana taunawa. Yama rasa abun cewa.

Hannun sa ya saka ya gogo kitchen cabinet sai kura. Ya nuna mata.

“What is this?? Ahlam… Wannan wane irin rayuwa ce uhm? Kalli datti please.”

“To aiki ya mun yawa. Ance zaa bani me aiki ka hana… Zan kashe kai na da aiki ne?”

Iskar bakinsa ya furzar mai matukar zafi. Cike da kosawa yace,

“Ina almajiran da ke miki komai??”

“Ba dai komai ba. bayan ka hana su dinga wanke duk wani plates da sauran kayan abincin dazaa zuba maka.”

“Lord! To Hakan shine laifi Ahlam? Nagaya miki ba sau daya ba. Ni mutumi ne me tsantsami. Alla ya sani, Bazan iya cin abinci da plates da sauran abubuwan da suka wanke ba. Almajiran dake wari suna tsami. Komai tabawa suke da hannun su basa wankewa. Haba Ahlam..wannan wane irin rayuwa ce? Mu biyu ne fa sai baba Mai gadi. Wane abu muke batawa da harsai almajiran ne zasu wanke. Just 3 of us… Haba Ahlam…”

Qunqumi ta shiga yi bata sake ce masa komai ba. Ya gyada kai kawai yana girgiza shi cikin takaici.

“Akwai abunda kike bukata ne da babu anan din?”

“Bakomi .. sai dai ko recharge card..”

“Oh ya rabb… Ni banga abunda kike da kati ba Ahlam sai renewing data plans shi yasa na yi deactivating wifi na gidan nan. Gaba daya 300gb ke kika karar da shi cikin kwanaki .. ”

“Noo. Ina kiran yan uwa mana…”

“Ba dai yan uwa ba… Harda kawaye. ”

“Bushra ce kawai. Kuma ita ai bestfren dina ce.”

“Ta fini muhimmanci ai awajen ki na sani… Bakya boye mata komai.”

Ko ajikin ta. Da abunda ya fada sai ca tayi

“Itama bata boyemun komai. Human diary din juna ne mu.”

“To ki zauna kina biye mata… Naga ba aurene da ita ba. She’s much less busy than u ahlamm.. That aside yau su Maa zasu zo kinsani ai. Kuma kinga ai ba zasu zo su tafi ba ba tare da sunci abinci ba. Da snacks and drinks haka.. Me zaki dafa musu?”

Bata ce komai ba. Ta yi shiru. Idanunta akan wayar da ke hannun ta. Tanata latsawa

“Ahlam….”

“Naam…” Ta amsa da sauri tana daga kai

“Magana nake miki … Dan Allah ki rage danna waya … ”

“Me kace?”

“Nace me zaki dafawa su Maa da zasu zo. ? Da su snacks haka da drinks?”

“Tab…”

“Pardon …?”

“Gaskia sai dai ko babbar me aikin Maa dinnan tazo ta dafa abincin.”

“Ke meyasa ba zaki ba.?”

“Ban iya ba.” Ta amsa shi kaii tsaye.

Ya sake jan leban sa ya ciza. Kafin ya sake cewa da ita,

“To drinks fa akwai? Zasu isa?”

“Eh… ”

“Tohm bari naje na dawo ..”

“Alright….” Ta amsa shi. Ta juya ta zauna taci gaba da danna wayarta.

Haka ya shiga mota ya nufi gidan su kai tsaye. Zuciyar sa nata tafasa. Ya kasa gane kan Ahlam. Tamkar ba mace ba? Ba sirri. Ba ladabi. Ba tarairaya. Ba tsafta… Ba godiya. Hakika babun ta tayi yawa.

Haka ya karasa gidan su yanata tunani ya saka wannan ya ware. Yana karasa parking ya shiga ciki bakinsa dauke da sallama.

“Wa’alaykm Salam…”

Tsugunna wa yayi har kasa ya gayshe da mahaifiyar tasu Haj Hameedah. Ta amsa da fara’a.

Lura tayi da yanayin sa. Sannan tace,

“Ga abinci can a dinning… Ko zaka coi.”

“Tohm Maa….”

Ya mike da sauri ya zauna akan dinning sai daya cika uwar kashin sa tukun sannan ya koma ya zauna akan kujera.

Ta sake tambayar sa kamar koda yaushe gamin yadda ya dan rame. Idanuwan sa tubarkaAllah sun sake manyanta.

“Akwai wani abunne?”

“A’ah Maa…” Ya bata amsa tamkar ko da yaushe

“Ya Ahlam din… Lapiar ta kalau?”

“Alhamdulillah….”

“Masha Allahu…. Yau mukace zamu kai ziyara kuwa. Amman sai an jima ”

“Eh… Insha Allah ” ya fada yana lankwasa hannuwan sa. Hade da shafa keyar sa.

“Akwai wani abunne?” Ta sake tambayar sa. Don tasan halin sa da zurfin ciki. Amman dai a matsayin ta na mahaifiya ta hasaso akwai yar tangarda a zaman sa da Ahlam

“Dama…Ahlam dince tace ko zaa kai me aiki ta tayata abinci…”

“Ta tayata ko ta mata?”

“Ta mata….”

“To gaskia dai kaga nan gyara suke tamun. Kuma Hadiza itace karfin aikin wallahi. Sai dai ko na tambaye ta idan Waheedah na nan sai taje..”

“Waheedah kuma Maa?”

“Eh Waheedah… Ai ta iya girke girke yarinyar nan. Sai ta mata din..”

“Tohm.” Ya amsa badan ya so ba.

“Hadiza… Hadiza!! Hadiza!!”

“Naam hajiya…” Ta karasa da sauri tayi gurfane agabanta.

“Dan Allah Waheedah na nan kuwa? Wai Ahlam ai kingane ta ko?”

“Kwarai na game ta… Wadda akayi bikin su ko?”

“Yauwa ita… Idan anjima ne zamu je gidan . Har da ke ma insha Allah. To shine takeson a ara mata wadda zata mata girki. Na yaba da hankalin Waheedah da kuma fasaharta na iya girki. Ba matsala taje?”

“Babu……Hajia. Tana makaranta. Amman nasan an kusa tashin su. Tunda yau jumu’ah….”

“Yauwa masha Allahu… Ai kace kasan makarantar ko. ? Ko ku tafi da Nassem ya muku rakiya. Da Nadra na nanne sai taje . To sai watan gobe zata dawo ”

“Nadra an sha hutu kam.”

“Tabbas ana kan sha ma. ”

“Shikenan Hadiza je ki ..”

“Tohm Hajia.”
Umma Hadiza ta miqe ta koma kitchen

Shi kuma suka cigaba da zaman kurmaye. Sai da Maa ta tashi ta kira Nassem .

Wajajen 11 da mintuna suka dauki hanyar makarantar su Waheedah. Ba jimawa kuwa aka tasa su

Nassem ya shiga da kansa makarantar aka nuna amsa ajin su Waheedah bayan ya tanbaya.

Suna gaban me youghurt yana yanka musu na 20 kowannen su

“Waheedah….”

“Naam…” Ta juya don ganin me kiran na ta.

Nassem ta gani a tsaye yana kare fuskar sa. Saboda ranar dake dallare shi

Karasawa tayi wajen sa tana murmushi.

“Yau kai ne a makarantar mu?”

Dan murmushin shima yayi kafin yace,

“Rakiya nayo ma.. Ni yanzu zan koma gidah. Zaku sauke ni.”

“Ni da su wa?”

“Ke da akiey… Ya Zayn.”

Yana karasa fada gabanta ya yanke ya fadi. Mumuguncin mutumin nan me zatayi masa.?

“Me zan masa?” Ta tanbaya batare da tasan ta fito ha.

“Kede muje… Sa ce ki zamuyi..” suna saka dariya baki dayan su .

Har mota suka isa. Nassem ya hide mata ya shiga ya zauna. Gabanta na tsananta bugawa. Juyawa yayi ya kalleta. Fuskar sa a daure.

“Ku sauke ni a kwanan layin mu. ” Cewar Nassem.

“Alright…..”

Har kofar layin suka sauke shi. Ya sauka har ya tafi. Zayn bai ja motar ba. Waheedah kuma bata tanka ha. Ya juya ransa a bace

“Ke waye driver din ki? Common dawo gaba ki zauna….”

Ta bude da sauri ta koma gaban ta zauna. Tana gatsina fuska. Murmushi ya so kufce masa dakyar ya danne suka dauki hanyar gidan sa.

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply