Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 43


Farhatal Qalb 43
Viral

PG:43__

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_

__
A hankali ta shiga bude manyan idanunta. Ta sauke su akan Umma Hadiza dake zaune tana zuba sukari acikin kunu .

“Kin tashi…..?”

“Eh…. Umma.” Ta miqe tana salati.

“Na so makara …”

“Ai da naga kince kina hutu (al’ada) shi ya sa ban tashe ki ba.”

“Ai ko na samu bacci . Godia nake Umman mu. Barka da safiya.”

“Barka ka dai Waheedah ..”

Kwandon sosan wankan su ta dauka da hijabin ta da ke jikin kyauren kofa

“Bari na watsa ruwa .”

“To afito lapia..”

“Aamin Umma.”

Ta fice ta shiga cikin bandaki. Bandakin akwai kan famfo da ake amfani da shi. Nan da nan ta tara masa bokiti ya cika ta shiga yin wanka.

Sai data gama tsaf ta janyo auduga ta saka . Kana ta sauya kayan . Daga nan ta sake tara ruwa ta dauraye wanda ta cire. Igiyar da ake shanya a baya taje ta shanya.

“Waheedah…”

“Naam gwaggo …. Ina kwana?” Waheedah ta sunkuya ta gayshe da gwaggo haule da ta futo daga cikin daki.

“Lapia kalau Waheedah . Kin tashi lapia?”

“Alhamdulillah gwaggo…”

“Masha Allah….”

“Gwaggo kin fito….?”

“Eh Hadiza…”

Suka sake gaysawa bayan ta asubah da sukayi. Dakuna hudu ne agidan. Guda daga ciki da ke gefe shine wanda Umma Hadiza da Waheedah suke kwana acikin sa.

“Har kinyi wankan?”

“Eh na dauraye kayan dana cire ma.” Cewar Waheedah.. Hannunta dauke da man shafawa na mai gurguwa.

Dan murmushi kawai Umma Hadiza tayi kafin tace.

“Zai sandare fa ..” ta fada tana mai mata nuni da kunu da kosanta.

“Ai kuwa bari na zauna…”
Ta janyo shi gabanta bayan tayi bismillah. Tashiga hadawa tana ci.

Tana karasa ci ta tattara yan kwanukan ta wanko su tas ta kife. Ta dauki tsintsiya ta share gidan baki daya.

“Sannu yar albarka…. Allah ya miki albarka Waheedah .”

“Aamin gwaggo…”

Turaren shafawar ta ta dakko bayan ta koma daki. Nan da nan ta murje jikinta da shi. Ta tsurawa kwalbar idanu . Yayin da idanunta suka cika taf da hawaye. Yaya Kamal kawai take tunawa.

Shi ne mai saya mata turaren. Da mai sayarda turarukan ya kawo layin su. Inde yanada kudi zai ce ya mata hadi a kwalba rabin shashi.

“Tsayuwar me kike yi ne?” Umma Hadiza ta tambayi Waheedah ganin ta chake a tsaye.

Waheedan tayi hanzarin goge idanunta gudun kar ta karyawa Umman tasu zuciya idan taga tana kukan.

“Ba komai abu na gyara…”

“Ko nayi gaba ne?”

“A’ah gani nan….” Ta fada da sauri hadi da zura hijabin ta .

A tare suka fita daga cikin dakin. Ita zata wuce makaranta. Ya yin da Umman zata tafi gidan aikinta na the Adams family.

“Har kun shirya?” Gwaggo haule ta tanbaye su. Fuskarta kumshe da fara’a.

“Eh gwaggo ..”

“Eh….”

“To Allah yasa ku fita a sa’a. Tsautsayi da asara Allah ya kare ..”

“Aamin gwaggo …”

“Aamin..”

Har kofar fita ta bisu tanata addua. Ta Kuma dankawa Waheedah nera hamsin kamar ko da yaushe

“Gwaggo bakya gajiya? Angode Allah ya saka da alkhairi.”

“Nagode gwaggo .. Allah ya kara budi ”

“Aamin kuyi sauri mana.”

Suka tafi sunata doka mata addua. Ita kuma ta koma ciki tana murmushi.

Adaidata suka hau ya kai su har bakin kofar jijjigaggen gate din layin the Adams family.

Suka sauka suka shiga cikin layin . Tsit ba hayaniya sai kukan tsuntsaye da kadawar bishiyu.

“Ki hanzarta Waheedah… Allah yabada saa da nasarar karatu.”

“Aamin Umma….”

Ta shiga cikin gidan. Ita kuma Waheedah ta miqe zuwa makaranta.

Da sauri ta shige cikin makarantar tasu. Daga wasu biyu bayanta aka fara tsaron latti. Ta sauke ajiyar zuciya ta karasa ajin su.

*GIDAN MALAM NALADO*

Marka ce a gwaggafe ta saisaye zani tana mai taya Deluwa jifar danwake a kan wuta.

Inna Sa’adatu ta fito daga bandaki kenan. Taa hango sabuwar butar data saya agaban Deluwa . Akan idanunta deluwan ta dauka ta rage wutar itatun gefe .

“Kan babban bala’in can …” Ta surfa ashariya hannunta akan bakinta

“Menene Sa’adatu …?” Marka ta tanbaya tana kallon ta.

“Nifa na gaji da cin kashin da ake akai na… Deluwa shara ce kawai tayi ragowa da zaki kwakwaso ki zubata akai na. Ko ki daura kwanon abincin ki bisa kai na ki ci . Wane irin renin hankali ne wannan iyye? Wabillahil lazi sanyi nayi. Ki tambaya kiji. Da mutunci yayi gabas. Yamma nayi ”

Deluwa ta tabe baki . Chas bata ce ba. Sai ma karban kudin wani yaro da yazo siyan Dan wake tayi. Tace ya jira ta zuba masa.

“Wato ga sauran kashin baqin duwawun ki … Ina magana kinyi banza da ni ”

“Ah… Wai menene ? Deluwa meke faruwa.?”

“Wallahi Marka bansani ba. Inaga da hannun hagu ta tashi…”

Inna saadatu ta sake bude baki. Ta kalli butar ta maqe maqe a hannun Deluwa sai kace tata. Ta riqeta gam. Hakan ya sake bakanta ran inna Sa’adatu.

Ta cire dankwalin kanta tayi damara dashi a kugu. Kana ta bude baki ta saki kukan kura. Zatayi kan Deluwa Marka tayi hanzarin rikota.

“Ah menene ya same ki ne Sa’adatu? Menene hakan fisabilillahi… ?”

Inna saadatu taja tsaki. Ta shiga kicinyar kwace jikinta daga riqon da Markan tayi mata.

“Ci ka ni Marka .. ci ka ni. Ina ruwan ki?”

“Ina ruwana. ? Haba Sa’adatu ”

“Yo ai gaskia ne… Tunda matar nan tazo gidan nan ke da yayan ki kuke shisshige mata saboda tana bar muku kanzon tukwane kuna kankarewa.”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun… Sa’adatu ni ki ka maishe wa mai maula? Me kike nufi! Kinsan kuwa maganganun da ke fitowa daga bakin ki Sa’adatu?”

“Na sani sarai. .. karya nayi? Ba haka zancen yake ba?”

“La… Zahara’u kina ji?”

Zahara’u dake chuda kan ta da kumfan los batace komai ba. Ta cigaba da abunda take yi .

Inna Sa’adatu ta bangaje riqon da Markan tayi mata. Ta nufi Deluwa gadan gadan . Batayi aune ba jikake tassssss.

Ta wanke fuskar Deluwa da mari. Bata ajiye hannu ba Deluwa ta mayar mata da biyu kwarara tas. Kasss. Zafafa . Wadanda suka sa inna Sa’adatu jiri ta dafe bango tana mai bin Deluwa da kallo.

“Kan babban bala’in can .. Ni kika mara?”

Deluwa taja tsaki. Ta gyara tsayuwar ta tana girgiza kafa.

“Mari na kikayi na rama… Da guzurin sauran dayan . Yana nufin ke ba tsarar cacar baki na bace….. Akan wane dalilin zaki mare ni! Rainin har ya wuce ga baqaqen maganganu ya koma kan mari? Ba kanwar lasa bace ni. Ki bini a sannu.. ”

“Haka kikace?” Cewar Inna Sa’adatu. Ta cika tayi fam

“Eh haka na ce… Ko kina da ja?”

“Zaki san kin debo ruwan dafa kan ki ..” Inna Sa’adatu ta fada.

Ta duka ta dauki kwabin danwaken da ke gaban Marka ta kwalalar da shi a kàsa.

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun….. Ke Sa’adatu.” Marka ta fada ganin ta asar da saadatun tayi….

Dariya ta sheqe da ita. Kafin ta juya saitin Deluwa. Ta daga yatsanta tana mai nuni da kwabin danwaken data malalar a kàsa. Cikin farin ciki da nuna isa ta shiga cewa,

“Wannan shine tukwicin dana baki…Akan sabuwar buta ta da kika dauka kike rage wuta da ita ..Gobe ma kya kara daukar abunda ba naki ba.”

Tana rufe baki Marka ta shiga tafa hannuwan ta tana dafe habarta da dayan hannun.

“Wannan butar fa ni Marka da girman Allah ni na dauka na bawa Deluwa… Wallahi yarinyar nan sam batasan ta waye ba. Ni ce na dauka na bata…”

“A hayye nanaye … To kinja mata….. Na meye zaki dauka mun buta? Kuma ma ni ba yadda zan ba. Tunda buta dai a hannunta na ganta tana rage cin wuta.”

“Amman dai Sa’adatu baki kyauta ba..Asarar nawa kika yi mata akan buta?”

“Kiji ki Marka da wani zance… Ni ansan nawa na sayi tawa butar? Akan wane dalilin zaa dauka mun? Saboda kun hada dadi shine zaki fara wasu zantuka.. Ni ba Hadiza ba ce. Ato.”

Tana karasa fada cikin fushi ta sunkuya zata dau butar a kàsa. Deluwa ta riqo butar itama. Suka daga kai suna kallon junan su a duqen kafin Deluwa taaaaaa…….

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply