Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 41


Farhatal Qalb 41
Viral

_PG:41_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA…_

___

*Waheedah* na tafe akan hanya tana mamakin maganganun Haj Hameedah. Su kuma haka Allah ya yi su da kaunar mutane? Kyautatawa da sanin ya kamata?

Ta sauke zuciya tana mai kambama dattako irin na Hajia Hameedah. A haka har ta karasa unguwar su

Kai tsaye ta wuce gidan Najan Isubu. Bakinta dauke da sallama ta shiga. Najan na share tsakar gidan.

Da sauri Waheedah ta karbi tsintsiyar bayan tayi sallama.

“Da kin basshi Waheedah..”

“A’a aunty zan karasa.”

“Toh sannu da kokari. Allah ya saka da alkhairi…”

“Aamin Amin”

Waheedah ta tattare tsakar gidan tas ta zuba dattin a shara. Sannan ta isa ga wata jarka ta tsiyayi ruwa ta wanke hannuwan ta da wani guntun sabulu data gani a gefen buta.

“Zo ga abinci Waheedah..”

“Wallahi a koshe nake aunty…”

“Abar marmari ce… Shinkafa da wake. To bari dai na zuba miki ki kai wa Yayan ku da Najib… Ya ya jikin na su kuwa? Ina tason shiga idan na kintsa komai ..”

“Tom aunty… Angode. Allah ya saka da alkhairi. Da sauki. Na baro su a gidah ”

“Amin Aamin..To Alhamdulillah”

“Aunty daman Umman mu ce ta aikoni wajen ki…”

“Tohn Allah sa muji alkhairi Waheedah.”

“Aamin … Dama dazu ne da safe Marka ta zo da wasu samari su biyu. Na san su ma …”

“Kwarai na ji zancen dazu a shagon Na’Ateeku. Fandau na fada. Kinsan uwar guntsi fetsi ce ”

“Eh… Tohm shine wai Markan zata bada hayar dakin. Tace na tattare kayana.”

“SubhanAllah…. Wallahi da naji suna zancen a shagon. Bata fadi wani daki bane. Da girman Allah na dauka dakin dake waje ne… Kai Marka batada kirki wallahi. Yanzu ya ake ciki…?”

Waheedan ta sheda mata komai ba abunda ta bari. Ta karkare da,

” Shine bayan na sanarwa Umman tace na gaya miki . Ko da akwai abubuwan da zaa tsitstsinta a sayar.. Tace dai na gaya miki. Dik abunda kika yanke yayi.”

Najan Isubu ta sauke zuciya tana matsa hannuwa. Cikin zuciyar ta kuwa tattare yake da tunanin yadda zata bullowa lamarin. Saboda gudun sharrin Marka ..

“Shikenan Waheedah… Allah ya dafa mana, Aamin.”

“Amin aunty ”

“Dauki abincin kije… Zan biyo sahun ki insha Allah … Allah ya dafa mana ya kawo mana mafita. Kije gani nan. Insha Allah.”

“Tohm Aunty…”
Waheedah ta dauki kwanon abincin dake kamshin man kulli da albasa. Gefe daya kuma kamshin yajin tafarnuwa ne yake tashi.

Ta fice daga gidan bayan tawa Najan Isubun sallama.

Gidah ta nufa. Ta shiga bakin ta dauke da sallama.

Yaya Kamal na daga gefen dakin su a zaune ya tsakure. Yayinda Marka ke ta kai da kawowa a cikin dakin Umman tasu. Wanda ya zamana na waheedah a yanzu.

Ta gama fito da kwanuka da wani kwali babba da kayan su ke a ciki. Da sauri waheedan ta ajiye kwanon abincin agaban Kamal.

“Gashi nan ku ci Yaya .. Kai da Najib. ”

Marka ta watsa mata wani banzan kallo tana mai nuna dakin da yatsanta daya.

“Shiga ki kwaso sauran tarikicen kayayyakin ku. Kin zo kin tsaya qerere a kai na saboda rashin girmamawa ga nagaba da ke. ”

“Kiyi hakuri…” Ta fada a raunace. Kafin ta ajiye yar jakar ta a gaban Kamal ta shiga dakin da sauri.

Dan wulaakancin Marka baki daya ta hautsina dakin. Wasu ababen fashewar baki daya sun fashe a tsakiyar dakin. Sauran tsakin dafawar su da wani ragowar manja baki daya Marka ta antayar da su a dakin..

Waheedah ta karasa fitar da komai ahankali. Wata drawer dinsu ce da kayan su ke ciki ta kasa janyota. Gashi hatasan kiran Yayan su. Ganin ba lapia ce dashi ba.

Tanata kiciniya sai ga Najan Isubu ta shiga tanata rangajin rangada sallama .

“Ko bakwa ji ne inata salamu alaikum.?”

“Yo sallamar ce kikayi ta iya cikin ki… Kina rowar buda baki. ” Marka ta fada tana yamutsa fuska

“Tuba nake uwar kowa. Marka tsohuwa mai ran karfe .. kowa ya ja da ke juji ne….”

“Najan Isubu manyan kasa. ”

“Wane ni ga ku? Tuba nake . Fatan na same ki lapia?”

Marka ta shiga busa hanci da daga kai. Jin yadda Najan Isubun ke fadada mata kai da washin da take mata. Ta dan yi yatsina. Kafin ta gaftari ragowar goron hannun ta tace,

“Lapia Lau… Ya Isubu kalau yake idan kun waya ko?”

“Alhamdulillah Marka .. Yama gaysar da ku.”

Naja ta karasa fada hadi da yaye yamfadin kofar dakin da Waheedah ke ciki. Ta zura kanta tana duba komai.

Shigewa ciki tayi. Ta tsaya tana bin dakin lungu da sako. Gabas da yamma.

“Dawo ta nan ki dauke wadannan. Bar daukar kaya masu nauyi kina budurwa kinji ko?”

“Tohn aunty …” Ta karasa fada hade da sunkuyawa ta debi kayan da ke bayan kofa.

Najan Isubu taja mayafi tayi madaurin kugu da shi. Ta shiga jan drawer a hankali har ta futar da ita daga dakin

Sannan Waheedah ta tayata suka karasa fito da sauran kayayyakin. Shigar Najib kenan gidan. Najan Isubun ta sanya shi ya curo yamfadin kofar dakin da aseberin da ke jikin window din dakin.

“Kayan sawar ku ne anan din ko…?”

“Eh …”

“To kwashe su ki zuba acikin wadancan Ghana must go din.”

“Toh..”

“Yauwa bara na leka na kira dan gwangwan din… ”

“Tom aunty…”

“Marka zan wa dan gwangwan iso…”

Bata tanka ta ba. Tayi kwafa dai kawai. Ganin hakan ya sanya Najan Isubu fita ta yiwa dan gwangwan da zai sayi kayan iso.

Ya shigo da sallama. Ya gayshe dasu. Kana ya shiga kallon kayan yana taba wasu daga ciki don jin ingancin su. Bayan ya gama gani duka.

Najan tace su fita. A wajen sukayi maganar kudin kayan. Baki daya ya saye su dubu biyar da dari hudu da hamsin.

Sauran yan kayayyakin nasu Waheedah ta mayar dakin su Yaya Kamal.

Kudin kuma Najan ta riqe su a hannunta bayan ta basu ajiya sun ki. Kan zata kaiwa Umma Hadizan da kanta.

××××

Haka rayuwar ta cigaba da garawa. Kwanakin Waheedah 3 agidan Najan Isubu. Da asubah take komawa wajen su Yaya Kamal .

Kudin kayan da aka sayar. Umma Hadizan ta baiwa Najan Isubun dubu daya dakyar ta karba

Sauran kudin kuma ta barwa su waheedan a hannun su. Saboda karin kumallo da sauran abubuwan dazasu bukaci kudi na yau da kullum.

Sati daya kuwa da tashin Waheedah. Wata mata ta tare adakin. Bazawara ce dake sana’ar abinci da zobo.

××××××

Najan isubu da kanta bisa jagorancin gwaggo haule suka samu Marka da maganar karbar Waheedah . Marka tace batasan zance ba.

Ta gwammace waheedan tayita karakainan neman matsugunin kwana amman bata amince tafiyar ta ba baki daya. Bayan ba wani abun take mata ba. Hassada ce zalla take yi. Don kada waheedan ta je inda zata huta taci cima mai dadi…

Hakan ya sanya su Umma Hadiza suka dakata da zancen. Har yazamto ma Umma Hadizan ta dakatar da zuwan Waheedah gidan na su the Adams family saboda gudun kar Moha yayi kuka.

Yayinda rana ke zama yammaci. Yammaci ta zama dare. Dare ya waye. Lalle Allah buwayi ne gagara misali.

Ranar wata sanyayyar juma’a da asubah. Bayan Najib ya tafi masallaci. Waheedah Kuma na tsakure a daki wajen Zainab suna kwance.

Haka kawai waheedan tun kafin safiya ta nemi bacci a idanunta ta rasa. Yayinda gabanta keta faduwa.

Tana idar da salla tadauki kwano don siyo musu yar tsala da kunu.

Najib ya dawo daga sallah. Ganin Yayan nasu har yanzu a kwance yake. Ga lokaci nata tafiya. Duk kuwa da bashida lapia shi ya sama bai tashe shi sunje masallaci ba saboda jikin nasa ba kwari gwara yayi agidah.

Hakan ya sa har ya kwanta akan katifar sa ya mike da sauri. Ya shiga tashin dan uwan nasa.

“Yaya…. An yi asubah fa. Ban tashe ka ba saboda naga baka jin dadi ne….” Ya shiga tashin sa shiru.

Yasake tattaba kafafun sa yana kiran dan uwan na sa.

“Yaya…. Ka tashi kayi sallah….”Nan ma shiru ba amsa.

Hakan yayi dai dai da shigar Waheedah dakin. Ta cire hijabin ta ta a jiye a kyauran kofa.

“Bacci yake har yanzu?”

“Eh….” Najib ya amsata a sanyaye.

Hannu tasa ta dago nasa da sauri hannun ya koma baya luuuu ya fadi.

“Yaya Kamal…. Yaya… Yayan mu.” Ta shiga tashin sa sosai tana kallon Najib.

“Daman haka yakan yi ..?”

“Be taba wannan nauyin baccin ba…”

Ta saka kunnenta a kofar fuskar sa wai ko zata ji numfashin sa. Nan ma shiru.

Da sauki jikinta na rawa ta fita . Malam nalado ne a tsaye yana gyara rigar jikin sa.

“Baba.”

“Naam Waheedah…”

“Baba zo kaga Yaya be tashi ba.”

Da sauri ya bi bayanta suka shiga dakin. Ya tattaba Kamal din. Ya mirginar da fuskar sa. Ya taba jijiyar wuyan sa da ta hannayen sa. Doguwar ajiyar zuciya ya sauke kansa a kasa.

“Baba menene?”

Bai ce komai ba. Ya janyo zanin gadon dake jikin katifar ya rufe Kamal din baki dayan sa.

Ya mike ya fuce zuwa kofar dakin Marka. Waheedah ta bishi. Yayinda gabanta ke tsananta bugawa da sauri da sauri.

“Ya akai me sunan malam?”

“Marka…. Allah ya yiwa…”

“Menene . Yayiwa me? Iyye?” Ta fada yayinda zaninta ke neman kuncewa.

“Kamalu ne Marka…. Allah ya masa rasuwa….”

._INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply