Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 39


Farhatal Qalb 39
Viral

PG:39_

*Karasa* karin kumallon nata tayi. Ta nannade sauran wainar yar tsalar ta doni dakakken kuli kulin daya sha hadi a baki. Kana ta kafa kai ta shanye ruwan shayi marar madara. (Ruwan bunu).

“Yaya Waheedah …”

“Na’am Najib.”

“Yauwa baki tafi ba ashe..? Ga shi inji Yaya Kamal.”

Ya daga asaberin da ke dakin ya shiga. Ya mika mata nera hamsin.

“Na meye?”

“Kudin makaranta mana.”

“Kai Yaya baya gajiyawa dai? Ai tayi yawa ma..” Ta amsa ta zura cikin yar jakarta.

Mikewa tayi ta goga yar jakarta a bayanta. Ta kalli kyakkyawar fuskarta acikin mudubi .

Tayi rama sosai saboda rashin Umman su a tare da su. Ba ita kadai ba su Kamal da Najib ma duk sun rame.

Safunan ta ta janyo da ke kan katifa. Ko’ina a dakin tas ta share ta gyara. Harda temakon turaren wuta na tsinke data kunna ta soka shi a bango.

Ta zura safar tana ta sauri gudun karta makara. Salama a kayo tun daga zaure. Marka da ke zaune kan turmi ta miqe da sauri

“Wa’alaykm Salam.Daga gidan gwangwan dinne?” Ta karasa tanbayar su tana mai sakace hakoranta da tsinke.

“Eh mune….”

“Yauwa ku shigo.”

Waheedah na kokarin janyo kofar zata rufo. Marka ta bangajeta tana,

“Ku shigo nan dakin ne…”

Matashin saurayin ya shiga yana duba cikin dakin kusurwa kusurwa. Shi kuma dayan da suke tare yana mai duba wajen dakin.

“Me gidah ya ne…?”

“Ah maza yayi fa. Mu chakata kawai. ”

“Toh ya ake ciki?” Marka ta tambaye su hade da zuba musu idanunta ba kakkautawa..

Dayan ya sake juyar da idanun sa ya kallo dakin. Hade da saka hannu ya dan daddaki bangon jikin dakin.

“Toh iya….Munga daki, Yaushe za’a kwashe kayan ciki?”

“Ke zo nan dan malafar gyatumin Hadiza. ”

Marka ta fada tana mai hararo fuskar Waheedah.

Waheedan ta isa gare ta kanta a kàsa. Yayinda kasan zuciyar ta ke bugawa sosai.

“Ga ni Marka.”

“Uhum. Nu na musu baki da ….” Kwas ta sakar mata rankwashi ta cigaba da cewa.

“Nuna musu baki da tarbiyyah na ce . ” Ta sake sakar mata wani bayan ta gama fada.

Kunya da zafin radadin zugin rankwashin da Marka ta sakarwa Waheedah ne yasa wasu hawaye sirara suka zubo mata daga idanu. Ta goge hawayen da kasan hijabin ta

Wadannan din da Marka ta jajibo har cikin daki . Ta kuma rankwashe ta agaban su ne. Abokai ne ga Ibrahim. Kuma majalisar su daya. Tare suke zama.

“Kiyi hakuri …” Ta rausayar da kai ta sake bawa Marka hakuri.

“Wuce ki tafi. Da kin dawo kuma ki tattare komatsan ki. Kisan yadda zaki dasu. ”

“Tom.” Ta amsa ahankali. Kana ta wuce makaranta kai tsaye.

Tana tafiya tana hawaye. Daya bayan diya suka shiga zurara daga idanun ta. Har sai data cire gilashin tukun sannan ta goge idanunta sosai kafin ta mayar dashi ta cigaba da tafiya.

A wurin shagon na fulani gab da shiga hanyar new gra shurah . Waheedah ta hango Umman su Hadiza na tafiya. Sanye cikin kayanta riga da zani ta dora da hijabi babba har kasa.

Da sauri waheedan ta cimmata. Tanata murmushi

“Umma ina kwana…?”

“Lapia Lou… Waheedah.”

Waheedah ta kasa boye farin cikinta na ganin Umma da tayi. Ta rungumeta . Fuskarta lullube da farin ciki marar misaltuwa.

Ita kanta Umma Hadizan a nata bangaren dadin farin cikin ganin waheedan itama ya mamayeta.

Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana mai danne hawayen da suke kokarin zubo mata.

Nan da nan kuwa Waheedah ta shiga zayyane wa Umma Hadizan dukkanin abubuwan da ke faruwa a gidan na su.

Umma Hadizan ta sake kwafar ta kan wasu abubuwan. Ta kuma nusar da ita ga hanyoyin da zatabi ta kaucewa duk wani tarzoma da kutungwila da ka iya tashi nan gaba agidan na su.

Suna tafe suna maganar har suka karasa new gra shurah. Dai dai kofar gidan na The Adams Family da suke hangowa hancin motar ya fito.

Wata zungureriyar mota jeep data ji kudi ta koshi ce ta fito daga cikin gidan.

Dr. Hameedah ce ke a kujerar driver tana tukawa. Rigar data dora akan kayanta kuma wata blazer ce white color . Ta yane kanta da farin mayafi.

Tana zuwa dai dai kusa da su ta tsaya da motar. Fuskarta kumshe da farin ciki ta zuge gilashin motar, Dukkanin su suka gaisheta cikin girmamawa . Ta amsa musu fuskarta a sake. Kafin ta dora da cewar,

“Ai munyi fushi Waheedah… Shikenan kin dauke kafan ki gaba daya? Moha kullun sai yayi maganar ki . Yayita tambaya kina iya.? Lalle a nemo ki. Idan na tambayi Umman ki sai tace kina gidah…. Uhm? Me ke faruwa ne Waheedah….?”

Waheedah cikin subul da baka tace,

“Ai Umma tabar gidan….”

“Banga ne ba…. Bata gidan kuma?”

Sai a sannan Waheedah ta gano ‘baram’baramar da tayi. Ta shiga mammatsa hannuwanta tana mai noke kai.

Umma Hadiza ta daga idanu ta mata kallon kin kyauta. Daga bisani tace,

“Kada mu bata miki lokaci Hajiya ..”

“Kar dai Waheedah ta makara. . Ba damuwa zamuyi magana insha Allah.Idan kin tashi daga makaranta ki biyo ta nan.”

“Toh Hajiya sai kin dawo .. Allah ya shi albarka ya bada sa’a Amin….”

“Amin Amin ”

Dr. Hameedah taja motar ta tatafi. Yayin da Umma Hadiza da Waheedah suka cigaba da tafiya.

‘umma kiyi hakuri .. wallahi bansan a fili na fada ba.”

“Sai a kori gaba… Ki tafi makaranta. Allah yabada sa’ar karatu “.

“Amin Yaa Rabbi..”

“Yauwa … Ya ya jikin su Najib da Yayan ku?”

“Allah ya kara sauki yasa kaffarane.”

“Amin Amin Umma ..”

“Najaatu na aiko muku da abinci ko?”

“Tana aikowa… Kusan kullum sai mun dumama munci washegari ma”

“Yauwa Alhamdulillah… Daman abunda yasa banason daya daga cikin ku yazo nan din ya karba. Ba komai bane fyace sai dai don kada tarzoma tataso. Shi yasaka nake cewa Najan ta turo Wanda zai riqa kawo muku.”

“Ana kawowa. Allah ya shi albarka….”

“Amin Yaa rabbi . Ai ba abunda zan cewa da su Hajia. Sai fatan Allah ya saka su gama da duniya lapia. Ya kuma kara musu arziki mai tarin albarka. Da wadatar zuci mai dimbin alkhairi….”

“Aamin Umma….”

“To shikenan sai kin dawo… Kada ki manta ki fa biyo tanan din.. Kamar yadda Hajia ta fada ”

“Insha Allah…. Umma.”

Sukaa rabu. Umma Hadiza ta shiga gidan The Adams Family. Ita kuma Waheedah ta miqe ta nufi makaranta. Tana tafe tana tunanin rayuwa da wasu qalubale na cikin ta ….

A haka har ta karasa makarantar. Ta tsallaka titi ta shige. Saura minti 5 a fara tsaron yan latti. Tana shiga kuwa ta sake numfashi na samun nutsuwar zuciyar bata makara ba…

×××××

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE__*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply