Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 37


Farhatal Qalb 37
Viral

37_
_____

*Marka* ta sha gaban sa da sauri. Zaninta har yana neman kuncewa. Saboda tsabar gigicewa da matotowar tashin hankali. Daurin dankwalin ta ya fado kasa. Duddugaggen farin gashin kanta ya bayyana. Gaba daya kan gaba da baya a gwaigwaye yake kamar konanniyar ciyawa.

“Adamushe… Bangane zancen da kake yi ba.?”

Tana magana ne hannun ta daya akan kullun zanin jikin ta yayinda dayan hannun kuma tana nuna zahara’u da shi.

Adamushe ya bushe da dariya har da kakatawa. Kafin yayi shiru ya sake murtuke fuskar sa ya na cin magani

“Marka da hausa fa nayi magana….”

“Haba ‘dan nan… Fisabilillahi! Akan wane dalilin zaka saketa? Saki har 3? Ana murna ta haihu .. Ta haifo da sarfacecen namiji. Kuna zaman zaman ku. Ko dai asiri ne dan nan?”

Adamushe ya sake yamutsa fuska. Yana mai duba agogon da ke wutsiyar hannun sa. Ya dago ya dubi Marka ransa a bace,

“Tambaya kike yi? Bana ra’ayin cigaba da zama da ita ne. Sannan bana kaunar ta. Dama can fanko ce aka lullube aka aura mun ita .. Maza take kulawa awaje. Tana hulda da maza. Ke Marka, Baki dayan yaran nan ba nawa bane. Ba jinina bane.”

Marka ta shiga hada hannuwa tana sallallami. Can ta dora hannayenta akanta tana surutai.

“Kai kira baban ku.” Inna Sa’adatu ta tura a kira malam na lado

“Wallahi Adamushe yarinyar nan duk inda nutsattsiyar yarinya ta kai. Zahara’u ta kai. Ko a gidan nan tun tana karama ma wallahi batada abokin fada. Ko musu ba’ayi da ita. Batada kwaramniya bare hayaniya. Da girman Allah wadannan yaran naku ne. K…”

“Kinga kiyi shiru da Allah . Sumumu ka sau. Micijin kaikayi sari ka noke…. Wannan yarinyar muguwar munafuka ce. Annamimancin ta yayi yawa. Ga makirci yar iska. A sati sai ta fita sau 6. Bata iya zama agida. Kwanakin baya makota ne sukayi taron dangi suka mata dukan tsiya gatanan ki tambayeta. Bashi kuwa data ciyo yafu a kirga. Du ta debe kayan ta ta sayar a kasuwar tsaye. Zamana da ita ya kare. Na fada zan sake nanatawa…”

Malam Nalado ya shiga gidan bakinsa dauke da sallama. Hannun sa dauke da wuka da raken da yake sayarwa. Fuskar sa dauke da damuwa. Tun tafiyar Umma Hadiza ga kuma wani tashin hankalin.

“Ina wuni..?..” Adamushe ya gayshe da malam na lado. A tsaye. Kafafuwan sa a jikin bango ya tokare

“Lapia Alhamdulillah Adamu… Ya iyayen kalau?”

“Lapia…”

“An samu karuwa Kuma … Allah ubangiji ya raya ”

“Amin. Allah ya raya muku ..”

Malam na lado yayi shiru bai ce komai ba. Adamushe ya hura iska bakinsa yana mai daga hannuwan sa sama,

“Na gama magana.. Yarinya dai da kuka liqamun gatanan na dawo muku da ita. Zamana da ita ya kare.”

“Ka tsaya Adamu muyi magana ta hankali… Zauna muyi magana ”

“A’a Malam. Babu wata magana anan gaba kuma. Na fada bari na sake nanatawa .. Na ce na saki zahara’u saki 3. Babu kome. Idan Allah ya bata miji taje tayi aure. Yara su uku gasu nan. Da jaririn ta a hannu. Duka ba nawa bane. Ba jini na bane wadannan yara. Ku tuhumi yar ku.”

Yana karasa fada ya gyara takalman sa ya fice. Malam Nalado ya biye bayan sa yana kiran sa.

“Adamu . Adamushe… Adamushe…”

Sam ko dar beyi ba. Tamkar ba da shi dinne ake magana ba.

Mutane sai bin su suke da kallo, Adamushen yayi gaba. Yayin da Malam Nalado ke bin sa a baya yanata sauri yana doka masa kira.

Waheedah na zaune akan katifa tana jiyo kukan aunty zahara’u kanwar mahaifin su.

Tabbas duk da ba kauna a tsakanin su. Da kuma mutunci a tsakani. Saboda gaba daya Markan ta dora zahara’un akan aqidar tsanar su baki daya da Umman su.

Tana jiyo komai. Lamarin ya bata tausayi sosai. Haka kawai cikin yan mintina ta tashi daga matsayin matar aure zuwa bazawara. Ga yara har 3 mahaifin su yace ba yaran sa bane

Ta goge hawayen ta da kasan mayafinta dake daure akanta. Ahankali ta tattaka ta fita zuwa tsakar gidan

“Ina wuni aunty zahara’u .?”

Bata amsa ba. Sai ma harara data banka mata.

Sum sum ta miqe ta koma daki ta zauna. Ta janyo plate din abinci tana ci tana korawa da ruwan gishiri har ta cinye baki daya.

Marka ta zama kamar mahaukaciya. Ta dora hannu aka tana karade tsakar gidan. Taje karshen bango ta koma can wajen zaure. Ita kadai tanata maganganu tamkar sabuwar mahaukaciya.

Yayinda zahara’u ke ife ife tanata birgima tana yawo. Jaririn na hannun inna Sa’adatu ta zabga tagumi itama..

“Ashe abunda yaron nan zeyi kenan yace zai kawota gidah? Wannan yaro wannan yaro Allah ka kwashe masa albarka. Uwar sa fureratu har ta koma ga Allah Ina binta bashin jaka biyu. Wallahi ban yafe mata ba kuwa. Da nace na yafe amman na janye yafiyar dan malafar kan uban sa. ” Marka ta ja kururuwa tana hawaye. Ta cigaba da cewa,

“Ya cuce mu..yaron nan ya gama da mu..”

“Wayyo Allah na ….. Marka .. wayyo Allah na” zahara’u ta kurma ihu tana jan kanta tamkar zata yage gashin kan ta.

Haka dai ranar baki daya gidan tamkar zaman makoki haka yayi. Tsit ba surutun kowa . Sai kukan jaririn . Ga makota da Marka ta shelantawa zahrau ta haihu sunata zuwa . Sam marka ta kasa sanar da su ai aure ya kare

Bakinta ya mutu murus. Ba maganar nan tata ta tsiya . Tayi tagumi taja kwafa. Haka tayita yi tana canza wajen zama.

Yadda taga rana haka taga dare. Batayi bacci ba. Tanata tunanin mafita. Zuciyar ta kuma na kitsa mata wasu abubuwan da dama.

××××××××

Gidah ya shiga ya sauya kaya zuwa wasu na yadi . Riga da wando. Bai saka hula ba, Sai gashin kansa daya taje kawai.

Ya feshe dukkanin jikin sa baki daya da turaruka. Kafin ya wuce sashen mahaifiyar su. Haj Hameedah.

Bakinsa dauke da sallama ya shiga cikin sashen .

Haj Hameedahn na zaune a parlorn farko hannunta rike da waya. Fuskar ta sanye cikin gilashin ta na kara gani

Ya durkusa har kasa ya gayshe ta cikin girmamawa ta amsa da fara’a. Tana yi masa kallon karin bayani. Ganin ai ance an kai angwaye gidan su tuni

Tuni ya gano kallon da take masa na menene. Ya sosa kasan keyar sa yana murmushi.

“Zan tafi….. ”

“Toh. Allah yayi muku albarka. Ya kara muku zaman lapia da kaunar juna …”

“Amin Aamin….”

Bata sake ce masa komai ba. Ta cigaba da danna wayarta. Amman cikin zuciyar ta addoin fatan alkhairi take musu da dacewar rahamar ubangiji….

Ya sake durkusawa ya mata sallama. Sannan ya fice. Kai tsaye ya shiga motar sa. Ya jima a zaune kansa akan sitiyari kafin ya tada motar da addua ya fuce daga cikin gidan. Kai tsaye ya wuce gidan sa. Wanda ke agaban na su Haj Hameedah a dayan layin mai titi wato new gra shurah phase 2.!!

*_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*

_(Where every flavour tells a story …..)_

*_By HAFSAT RANO_*
_(Mother/wife/writer)_

_08030811300_
_IG:Rano_scrumptious_meal_

_INA MA’ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL’ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_

_MU NA YIN:_

*_FUNKASO_*
*_ALKUBUS_*
*_SINASIR_*
*_WAINA_*

*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_*
*_COW TAIL/COW LEG (DAB’URI)_*
*_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*

*_LOCAL DRINKS:_*

_HIBISCUS (ZOBO)_
_GINGER_
_AMAANI FRUITY SHAKE_

_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY…._

_KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT…._

_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_

_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_

_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST….. DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _ASSALAMU ALAIKUM…_
_YAU MUN KAWO KOKEN KU KARSHE . MUN NEMO MUKU INDA ZAKU SAMU LUSH AND COMFY BUBUS CIKIN FARASHI MAI RAHUSA DA INGANCI_

_LUSH/COMFY BUBUS BY: MRS. ZP_

_08147243787_
_WHATSAPP:+234 904 998 9332_

_WADANNAN BUBUS SUNA DA MATUKAR LAUSHI KUMA A SAKE SUKE BABU MATSI_

_KALA KALA NE DA SIZES DABAN DABAN…KUMA KOWANNE IRIN LIYAFA ZAKU SAKA KUJE. IRIN RICHLY LOOKS DINNAN DA SAI AN KALLE KU AN SAKE KALLA SABODA KYAWU DA INGANCIN SU. BUBUS DIN A HADE SUKE DA MAYAFAN SU.. ZAKU KUMA IYA PAIRING DA WASU MAYAFAN DABAN_

_WADANNAN BUBUS ANA BADA SU NE AKAN FARASHIN SAYA DAYA DAYA KO SARI….. 12K AKAN GUDA DAYA. IDAN SARI NE KUMA 11K. WADANNAN FARASHIN KASUWA NE. DUK INDA ZAKU ZAGA KUDIN SU YAFU HAKA.. MUNA ARHA NE DON KOWACCE MACE TA IYA MALLAKAR SU._

_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KOINA A FADIN NAJERIYA DA KETARE .._

_ADIRESHIN SU: NA’IBAWA ZARIA ROAD, KANO.._

_IDAN ANJE SIYA ACE DAGA ZAFAFA NE. DOMIN MUN YABA DA KAYAYYAKIN SU. KUNSAN DAI BAMA TALLATA MUKU ABUBUWAN DA BASUDA KARKO_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA SAI COMFY BUBUS DIN MRS. Z.P_

——–

_FARHATAL QALB_
_(FARIN CIKIN ZUCIYA)_

_NA_

_NANA HAFSATU_

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply