Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 36


Farhatal Qalb 36
Viral

__PG: 36_

*Dakyar* Waheedah ke iya bude idanunta. Saboda tsananin yadda kanta ke sarawa. Kanta na mata madaukakin ciwo. Ya yinda gangar jikinta ta dauki zafi rau tamkar garwashin wuta.

A haka Kamal ya shiga dakin a daddafe don shima ba dadin yake ji ba. Ya nemi waje ya zauna akan wata kujera ta tsugunno.

“Sannu Waheedah…”

Bude idanun tayi da suke rufewa da kansu. Sunyi jawur da su. Sun kara furfutowa waje tubarkaAllah.

“Yaya Kamal…. Kai zan wa sannu. Ya jikin?”

“Da sauki … Alhamdulillah. Ya jikin?”

“Da sauki…” Ta fada tana mai cije labbanta. Ta miqe ta zauna dakyar daga kwanciyar da ta ke.

“Yanzu Najib ze kawo miki ruwan gishiri ki sha. Saboda karfin jikin naki .. Kin sha panadol din ko?”

“Ban sha ba… Zan sha yanzu.”

“Yana ina?”

“Gashi nan…” Ta nuna masa kan murfin samira. Ya dakko ya tashi ya tafi dakin su ya dawo da pure water guda 3.

“Ungo sha maganin… Wannan sai a hada miki ruwan gishirin ko . (ORS). ?”

“To Yaya … Ka koma ka huta.” Ta fada a wahalce

Ya danyi murmushi kawai. Yana dada kallonta sosai. Lalle Waheedah batata lapia sosai. Don bata kwanciya akwai kazar kazar. Bata taba cewa ta gaji akan aikace aikace.

“Mu idan muna kwance ba lapia Waheedah ba ki taba kosawa. Komai da komai yi mana kike yi ba gajiwa. Ubangiji Allah ya baki lapia ya sa kaffarane. ”

“Aamin Yaya…”

“Kibar kukannan haka kinji?

“Tohm …Yaya” Ta fada muryar ta na rawa.

Ba jimawa kuwa Najib ya shigo hannun sa dauke da leda baka. Ruwan gishirin ne sachet 3 aciki da kuma pure water rabin leda a dayan hannun sa.

“Dakko jug dincan ka hada mata. Ka ga ka fara dauraye shi tukun ka ji?”

“Tom Yaya.”

Najib ya debi ruwa a kwalla ya wanke jug din ya hada mata ruwan gishirin ya miqa mata.

“Ka da ki sha ruwa sai kin gama shan sa..”

“Tohm Yaya….” Ta amsa shi.

Kasan zuciyar ta ta tuno yayan nasu da tuni yanzu yana aiki a asibiti ko wata ma’aikata data shafi harkar lapia ko kamfani. Domin chew (community health extension worker) ne shi kafin ciwo ya kankame shi baki daya..

Har ya mike yar wayar sa mai torch light ta shiga kara a aljihun sa, Ganin number Najan Isubu ce. Hakan ya sa ya dauka da sauri. Ya kuma koma ya zauna

“Wa’alaykm Salam… Ina wuni? Ah Alhamdulillah wallahi. Waheedah? Da sauki gata ta dan zauna… Eh shima yana nan. To bara na turo shi. Mungode, Allah ya saka da alkhairi. Amin. Okay tohm ”

“Ka karasa hada mata…?”

“Eh. Gashi nan tana sha ma ”

“Yauwa. Kaje gidan Najan Isubu ka karbo abinci. Umma ce ta bata ta kawo mana..”

“Allah sarki Umma. Muna ran ta. Uwa mai dadi. Allah ubangiji ya saka mata da mafificin alkhairi. ”

“Aamin Yaa Rabbi .”

“Aamin.”

“Bara na dan watsa ruwa ”

“Tohm Yaya…”

Kamal ya fice zuwa bandaki. Yayin da Najib ya fice zuwa gidan Najan Isubu. Daki ya zama sai Waheedah ita kadai tana zaune. Kanta a sama.

Marka ta leka ta windown tana tabe baki. Kafin ta shiga ciki ba ko sallama ba re sannu

” A koke.”

“Naam Marka .”

“Ungo debo mun ruwa acikin nan…” Ta miqa mata wani bokitin karfe kato.

Waheedah ta cika da madaukakin karshen mamakin halin ko in kula irin na Marka. Yanzu yanayin da take ciki na rashin lapia haka zata fita ta ebo ruwa bayan ga su Zainab can tana jiyo karakainan surutan su.

“Ko ba zaki ebo bane? Yo naga ma fuskar ki a murtuke kaman zararriyar zakan ya. Zaki hau kai na da bugu ne?…”

Waheedah ta girgiza kanta da a’a. Ta miqe dakyar. Jiri na neman kayar da ita. Amman a haka dai ta daure ta karbi bokitin tana dafa bango. Har ta fice daga dakin.

“Mene nan? Gayyar munafurci.” Marka ta shiga bude kwanuka. Harda daga jug din ruwan gishirin da kalar sa tayi kaman lemo. Ta kwankwada zata sha banza ta dauka lemo ne. Da sauri ta fuce ta isa ga rariya ta amayar da shi tana tabe baki

Wani jiri ya kwashi Waheedah. Tayi sama dabas tayi zaman yan bori a kàsa. Nan da nan ta sa kuka. Ba wai kukan faduwar da tayi bane. A’ah kuka ne akan zallar kiyayyar da Marka ke nuna musu a cikin dukkanin jikokin ta… Sun zama saniyar ware acikin jikoki. Tsana ce ta ke musu mai yiwuwar fassarawa.

Kamal ya fito daga bandaki da sauri. Ya ajiye kwandon sosan wankan su a gefen daki. Ya nufi wajen Waheedah da ke sheme ta na kuka babu mai tanka mata. Ya dagata da sauri yana dudduba kafafunta da hannuwan ta.

“Ba inda kika ji rauni ko? Eh Waheedah.”

“Babu Yaya…”

“Me zakiyi da bokitin nan.?”

“Ruwa.. Zan debowa Marka.”

Ya dauki bokitin ya fice waje ya ebo ruwan ya kai dede kofar dakin Marka ya ajiye .

“Ba kai daya nake so ba …. Kai biyar nake bukata.” Ta karasa fada tana yatsina.

“Yaya zan ebo.”

“Keda baki da lapia. Barshi ”

“Uhm se an ebo dai. ” Marka ta sake fada hade da sakin guda.

“Wai ni Marka karfe nawa zamu tafi ne. Naga garin ya fara hadewa ” cewar Inna Sa’adatu.

Marka ta sheke da dariya tana murna . Farin ciki ya wanzu a fuskar ta sosai tace,

“Mai jegon ma ta kira wayar mai sunan Malam. Tace ko mai dare da yardar Allah zasu zo nan. Anan zatayi wankan ina tunani ”

‘ahto Alhamdulillah.. Allah ya kawota.”

“Aamin.”

Kamal ya cigaba da zubawa Marka ruwa. Har sai da yayi kai biyar tukun sannan ya ajiye bokitin. Ya koma ya temakawa Waheedah ta koma daki. Sannan ya shige dakin su. Saboda jikin sa har ya fara ciwo.

Marka ta debi ruwa tayi bandaki tana yan wake wakenta.

Ba jimawa Najib ya shiga gidan dauke da babbar kular abinci ya kai daki wajen Waheedah.

“Gashi …”

Waheedah ta daga kai ta kalle shi.

“Ku zuba ku ci…”

“Bari na kira yayan….”

Ya je dakin su ya kira Yayan na su. Dan har ya kwanta ma shi Kamal din yanata juye juye.

“Gani nan……” Ya fada a wahalce.

Ko da suka koma dakin suka bude kular, Waina ce da funkaso da sinasir da alalan cikin ganye. Sai miya dauke da nama fal a kulle a leda baka babba

“Samo wuri ka zuba shi …”

“To Yaya.”

Najib ya samu mazubi ya zuba komai. Suka debi nasu suka bar na waheedah. Sauran kuma zasu dumama suci.

Fitowar Marka daga bandaki kenan. Zahara’u yar autar Marka. Wadda ta haihu tace zata biyo gidah komai dare. Ce ta shigo gidan

Tana gaba yaran ta 3 wani na bin wani suka biyo ta a baya. Ita kuma da jaririn a bayanta. Yayinda mijin na ta Adamushe yana bayan su yana muzurai.

“Oyoyo oyoyo…” Yara sukayi kan zahara’u da yaranta anata murna.

Marka ta karbi jaririn tanata masa wasa.

Adamushe ya harde kafafu yaci magani. Fuskar sa ta cika tayi fam tankar zata fashe cikin kolokuwar bacin rai . Ya saita hannun sa setin kan fuskar Zahara’u tamkar zai waska mata mari yace,

“Na sake ta saki 3 ……. Babu komeee. Sannan wannan bakin jaririn da hanci hura hura da girman Allah ba ‘da na bane. Ba jini na bane. Na karkare miki zance. Wadancan ukun ma ban amince na waje na bane. ” Yana karasa fada ya yi hanyar zaure zai fuce …

_INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE__INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

*_FARHATAL QALB_*
_(FARIN CIKIN ZUCIYA)_

_NA_

_NANA HAFSATU_

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply