Daudar Gora Book 2 Hausa Novels

Daudar Gora Book 2 Page 94


Daudar Gora Book 2 Page 94
Viral

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (94)

 

*_MAAB LUXURY HOME._* _Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini. Ina uwar gida da Amarya, Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._

_____________________

………Cikin ƙanƙanin lokaci zancen haihuwar Iffah ya karaɗe ƙasar ruman baki ɗaya. Tuni farin cikin kowa ya bayyana, tare da addu’oi ga waɗan nan jinjiraye da ga bakin al’umma. Yayinda Tajwar Eshaan daya matsa a kai masa su ke can rungume da kayansa tsam-tsam a jiki. Jinsa yake a yau ɗin kamar wani sabon mutum, final shima dai ya zama Abbie. Ga yaran sun ɗakko kamanninsa sosai musamman ma mace kamar an tsaga kara an karya da shi, gara namijin yafi rinjaya da Iffah shi kuma. Da kansa ya tauna dabino ya basu tare da musu huɗuba.
Duk yanda yaso ganin Sohaa ɗin sa hakan bata yuwuba sai bayan la’asar tai barcinta ta huta sannan. Murmushi ta dingayi kanta a sinne saboda irin kallon nan na ƙasa-ƙasa da yake faman binta da shi. Duk sai taji kunya ta lulluɓeta. Har ya ƙaraso gaban gadon bata yarda ta ɗago ɗin ba sai da ya zauna a kusa da ita ya ɗago fuskar tata da kansa. Bai tsaya wata wata ba kawai ya manne lips ɗinsu waje guda. Sai da yayi yanda yake so da ita ya barta dan kansa sannan ya rungumeta yana jero mata daɗaɗan kalamai masu sanyi da ratsa zuciya da bata san yayi nisa a sani ba har irin haka. Jitai kawai idanunta sun cika da ƙwalla. Dan ita kanta bata san adadin ƙaunar da takema wannan bawan ALLAH ba zuwa yanzun. Tana jinsa daban a cikin daban a duniyarta. Shi ɗin na musamman ne a gareta fiye da yanda yake jinsa na musamman…

Lokacin da aka kaima Malikat Bushirat da har yanzu ake nan yanda ake babu abinda ke motsi sai kai da ido Jasrah baiwar ALLAH nata wahala da ita kuka sosai ta fashe da shi. Suko yara kamar sun san inda aka kawosu suka wani dage da tsanyara kuka tsiyau-tsiyau kamar ƴaƴan magena da yau mukasha bikin sunansu (Na manta ban faɗa muku ba magena ta haihu ƴaƴa hudu kowa sai ya kawo kayan barka haihuwar fari ce babu ɗaga ƙafa😂🚴🥱) kuka sosai suka dingayi har abin ya bama kowa mamaki, ana fita da su sukai shiru kuma kamar basu ba. Koda aka maidasu anan bama Malikat Haseenat da Iffah labari murmushi kawai Iffah tai batace komai ba. Garama Malikat Haseenat tsohuwar ƙwarai ta tofa kaɗan.
A can ko jikin Malikat Bushirat rikicewa yay sosai. Dan har sai da takai an kira Shahan-shan da Malikat Haseenat. Al’amarin kam yau dai bana wasa bane. Dan doctors da suka rufu a kanta ma dai sunyi iya ƙoƙarinsu amma bata bar jijjigar da ta dingayi ba, daga baya ma sai ga aman jini. Hankalin kowa ya tashi musamman Tajwar Eshaan, dan da kansa ya hau gadon ya rungumeta jikinsa ta dinga bulesa da aman jinin nan. Addu’a ya dinga tofa mata, ganin fa tafiyar mai tsaho ce Malikat Haseenat ta fara maimaita kalmar shahada ko za’a dace Malikat Bushirat ɗin ta karɓa. Hakan yasa suma sauran jama’ar dake a ɗakin suka dinga maimaitawa, Jasrah dai kuka take kamar ranta zai fita. Sai dai kuma ita rayuwa duk yanda kaso, bai zama lallai abinda kaso ɗin ya kasance a yanda kaso shi ba. Dan kuwa dai Malikat Bushirat ta koma ga UBANGIJI batare da ta iya neman gafarar koda ɗan cikinta tilo data jefa kanta a halaka domin haihuwarsa ba. Tayi mutuwa mai ban tsoro da tashin hankali, dan kuwa maimakon kalmar shahada da suka so ji daga bakinta sunan UWA ne ƙarshen ambaton ta cikin wani irin gurnani mai ƙarajin gaske daban tashin hankali. Wannan al’amari ya matuƙar kiɗima Shahan-shan. Dan jikinta na gama saki shima ya kife kansa akan fuskarta. Tsahon lokaci bai ɗago ba har sai da kowa ya fita a ɗakin Malikat Haseenat tazo tana lallashinsa. Sannan aka samu ya ɗago idanun nan nasa jazur matuƙa abin tausayi, sai dai baiyi kuka ba, ya jima yana kallon fuskar mahaifiyar tasa abubuwan data lissafa ta aikata na dawo masa tiryan-tiryan kamar yanzu take yinsu….

Masarautar gaba ɗaya ta gama rikicewa. Dan mutuwar nan kam ta daki kowa musamman da Malikat Bushirat ta zama tamkar wata tauraruwa a zamaninta a cikin gidan. Sai dai yanda mutuwarta tayi dai-dai da mutuwar kaf mutanen nan ƴan ƙabilar uwa abin ya bama kowa mamaki. Dan kamar waɗanda aka shayar guba kawai aka samesu duk a mace su kusan goma sha uku. Dama wasu sun ɗan mummutu ɗaɗɗaya. A yanzu dai kam Uwa kawai ta rage a raye. Itama ɗin dai sai a hankali dan duk ta ƙara wani irin yamushewa na tashin hankalin faɗuwa ƙasa da tai. Wai yau itace mai zaman kurkuku a cikin masarautar ruman kuma da ranta da lafiyarta tsahon watanni shida. Ai ko’a iya haka aka tsaya ta gama kunyata a wannan duniya.

Jasrah ce ta mata wanka tana kuka abin tausayi ita da yayarsu Badiha. Bayan an mata sutura aka fiddota Tajwar Eshaan ya jagoranci sallatarta tare da miƙata gidanta na gaskiya aka barta da halinta kuma. Dan ya rage ita da UBANGIJINTA. A yanzu kam. Wannan itace ranar da ya kama kowa ya kasance yana gudu a rayuwarsa. Dan ko kaƙi ko kaso sai tazo. Ko kai mutumin kirki ne kona banza ne ma dai sai tazo. Ko shekara dubu bisa dubu zakayi a duniyar sai tazo. Koka shirya ko baka shirya ba sai tazo. Yau dai gashi Malikat Bushirat ta tafi tafiya ta har abada. An shafeta an shafe babinta dama iyakarta kenan akan duk wani abin kirki ko ɓarna da zaka shuka a duniyar….
Tajwar Eshaan bai samu hawayen dake riƙe da maƙoshinsa sun zubo ba sai da yaje ya rungumi ƴaƴansa da matarsa sannan. Kuka yayi sosai Iffah na tayasa. Sai da sukayi mai isarsu abin tausayi. Ranar ma har zazzaɓi yayi dole Iffah ta kwana tare da shi da ƴan yaransu da sukaci sunan Ajwaad da Ajwaa (Dan su bawani al’adar suna a sati ɗaya suke ba ba irin ƴan 9ja bane😝). An dai yankama yara raguna da shanu akai sadaka a washe gari tunda ranar mutuwar Malikat Bushirat ta hana. Gida kam ya cika maƙil, ƴan gaisuwa da taya murnar haihuwa ta ko ina ketowa suke. Su Mamy (Daneen Ammarah) sun zo suka kwana itama da cikinta ɗan watanni biyar da wasu kwanaki. Da alama dai zancen Babiy ya tabbata. Ita da Ummu idan ka gansu abin sha’awa kamar yaya da ƙanwa. Sai ma shirye-shiryen bikin Hanash da sukeyi dan shikam ya koma ɗan ɗakin Mamy, Iffah dai na nan ƴar gaban goshin Ummun ta kuma autarta. Dan duk ƙurarta idan ta yaya Ummu dai, itace abokiyar shawararta itace abokiyar sirrinta. Sai an gama Mammy kanji da Babiy. Iyakarsu dariya idan na dariyane. Idan na fatan alkaicine kuma suyi addu’a. Iyyani da kaka kuwa ai dama tuni sun dawo cikin masarautar. Ko yaushe zaka sami Iyyani tare da Malikat Haseenat ne da ƙanwarta Yamma. Tsaffin sun matuƙar haɗe kansu sun zama iyayen kowa. Hakama Kaka da su Sayeed Fayzul-haq sun zama aminan juna dattijan ƙwarai kuma a masarautar kuma iyayen kowa har shi kansa Shahan-shan ɗin….

*_BAYAN WATTANI UKU DA HAIHUWAR IFFAH DA MUTUWAR MALIKAT BUSHIRAT (BIKIN AL’ADA)_*

Kamar kowacce shekara a wannan karon ma tarin al’ummar ƙasar ruman da kewaye sun cika birnin Dahab da akafi sani da DAULAR RUMAN tako ina domin gudanar da bikin wasan al’ada. Kowa ka kalla a wannan karon yasan wasan na musamman ne sannan ana gudanar da shine cikin tsafta da nutsuwa. Duk wani wasan ganganci da za’a iya rasa rayuka an kafa masa doka, hakama matakan tsaro tako ina an baza domin kare kowa da kowa. Duk wani boka ko ɗan bori ko malamin tsubbun an hanasu yin kowane motsi a yanzu. Dama yanzu kam dokane, in har aka kamaka to hukuncin kisa kawai ake yanke maka.
A yau kam Iffah taga mutane da yawa da suka kawoma Shahan-shan gaisuwa. Ciki harda Sir Fawzan da tuni yay aurensa. Tare da yaran Shahan-shan su Azaan da a yau kam sukaita faman sinne kai na kunyar abinda ya faru tsakaninsu da ita a shekarun baya. Ita dai murmushi ma ta dingayi, shi kansa uban gayyar Shahan-shan murmushin yaƙe yi dan kawai ba’a ganin fuskarsa ne. Su Ajwaa da Ajwaad sunsha addu’oi yau a wajen mutane. Duk da ma bawai kowa ake bamasu ba. Yaran sunyi ɓul-ɓul abinsu gwanin sha’awa. To mi yafi ransu suna samun kulawa da tattali da soyayyar iyayensu. Dan zuwa yanzu ma dai kam Iffah ta tattara inata-inata ta koma sashen Shahan-shan ɗin gaba ɗaya ita da yaranta. Dan yace shikam babu wani sashen matarsa da ban nasa daban. Idan ka ganta a sashenta sai in tayi baƙine ko yin wani abun dai tunda babu mai hurumin zuwa sashen Shahan-shan ɗin sai ita. Hatta da amintaccensa ma zuwa yanzu iyakarsa hawa na na uku ne kawai, idan ka gansa a hawan ƙarshen sai ƙwaƙwƙwaran dalili…..

★Alƙawarin ALLAH ya cika akan zartar da hukuncin su Miran Jasim da Miran Arshaan a yau. Dan kuwa wanda ya kashe dole ne a kasheshi. Hatta da malikat Bushirat Tajwar Eshaan ya gama yanke hukunci a yau ɗin zai zartar da hukunci a kanta irin hakan sai ALLAH kuma ya ɗauki ranta kafin zuwan yau ɗin. Sosai al’amarin ya girgiza kowa matuƙa, musamman ganin iyalan Miran Jasim ƙalilan ne a cikinsu suka koka saboda wahalar daya basu a rayuwa. Shi dama Arshaan ba’a ajiye kowa ba. Amma duk da haka Jasrah mai karyayyar zuciya sai da tai kuka. Al’ummar ƙasa sun taru wajen nema musu afuwar ƙarƙashin cigaba da zama a cikin kurkuku tsahon rayuwa. Hakan yasa duk sai jikin Tajwar Eshaan ɗin yay sanyi, dan shima yanajin ɗaci fiye da irin ɗacin da kowa ke ji kasancewar su kaɗai ne Uncle’s nasa makusanta da mahaifinsa da suka rage a duniya sai mata. Ganin dai jama’a sun dage ɗin kuma harda iyalan Sayeed Khairul-Bashar da kansu dana Sayeed Hifzur-rahaman ɗin suma yasa aka maidasu cikin kurkukun a bisa sassaucin ɗaurin rai da rai. To saima dai ta ALLAH dan shi Miran Jasim ma bawani cikakkiyar lafiya ce da shi ba. Hatta Miran Arshaan ɗin kansa kawai dai a rufe rufau ne.
Uwa kam da aka fiddo cikin sarƙa cike da ƙarfin iko kowa ke shelanta a kasheta!! A kasheta!!! A kasheta!!!. Kallonsu kawai take tana kuka da dariya da kiran sunayen gumakansu duk a lokaci ɗaya. A haka aka ɗaureta jikin ƙarfen. Mutane zasu fara jifanta da dutsina aka dakatar da su. Dan wannan aikin ba nasu bane na mai gayya da aikine da kansa tare da matarsa. Bayan lafawar kowa fiye da yanda ake buƙata Shahan-shan ya fito hannunsa na dama riƙe da na Iffah, na haggun rungume da Ajwaa da aka canjama gayu ita da Ajwaad. Da shi kuma ke a hannun Iffah. Masha ALLAH aka shiga ambata, dan a zahirinsa ya fito ga mutanensa babu wani shamaki yana son su gansa ya gansu. Haka itama Iffah duk jikinta a rufe amma fuskarta a bayyane ga al’ummar ƙasarta. Bayan sunyi gaisuwa ga al’ummar ƙasar su da fatan alkairi aka kawo kwari da baka na tsire Uwa da zasuyi. Iyyanni da Malikat Haseenat ne da ke tare da su suka amshi twins, yayinda Tajwar Eshaan ya kamo hanun Iffah a hankali cikin nasa yana kallonta ƙasa-ƙasan nan nashi ya tsayar da ita gabansa. Matsawa yay ya jingina jikinsa a nata tare da kamo duka hannayen nata biyu cikin nashi ya saka mata kwarin tare da ɗaga hannayen nasu a tare ya daidaita su sannan ya daidai mashin da zasuyi amfani da shi cikin bakar saitin manya-manyan idanun nan na uwa da ke kwasar dariya da kuka kamar sabon kamu………..✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

 

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply